Musulmin Biritaniya na adawa da ramuwar gayya kan nuna hoton Annabi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ji ra'ayoyin Musulmi 1,000 a wurare daban-daban a Biritaniya

Galibin al'ummar musulmin Biritaniya suna adawa da daukar mataki a kan mutanen da suka wallafa hoton da ke nuna Annabi Muhammadu (SAW), kamar yadda wani binciken jin ra'ayoyin jama'a ya nuna.

Binciken ya nuna cewa galibin mutane sun dawo daga rakiyar mutanen da ke kokarin fada da kasashen yammacin duniya.

Kashi 27 cikin 100 na Musulmai 1,000 da aka ji ra'ayoyinsu da kamfanin ComRes ya gundanar sun nuna cewa suna tare da mutanen da suka kai hare-hare a Paris.

Kashi 80 na ganin cewa bai dace ba a buga hoton Annabi.

[an error occurred while processing this directive]

Da aka tambayesu ko rikici da wadanda suka nuna hoton Annabi Muhammadu ya "dace", sai kashi 68 suka ce bai dace ba a kai musu hari.

Kashi 24 ba su amince ba, a yayinda sauran suka ce "basu sani ba" ko kuma suka ki ba da amsa.

Binciken da aka gudanar daga ranar 26 ga watan Junairu zuwa 20 Fabarairu, ya nuna cewar kashi 32 na Musulmin Birtaniya basu ji mamakin harin da aka kai wa mujallar Charlie Hebdo wacce ta wallafa hoton Annabi da kuma shagon Kosher a Paris.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Binciken ya nuna cewa kusan rabin Musulmin Biritaniya sun ce suna fuskantar bambamci saboda addininsu kuma kasar na rage kulawa da su, kuma da dama daga cikin Musulmin suna ganin cewa Musulmi na shan wuya wajen gudanar da ibada a Biritaniya.

Kashi 35 na ganin cewa al'umma Biritaniya ba su yarda da Musulmi ba.

Daga wadanda aka ji ra'ayoyinsu, kashi 95 suna biyayya ga Biritaniya, sannan kashi 93 na ganin cewa ya kamata Musulmi su bi dokokin kasar.

Kashi 20 na mata sun ce suna cikin fargaba a Biritaniya a yayinda kashi 10 maza suma suka bayyana haka.