Boko Haram: 'Reshe ya juye da mujiya'

Hakkin mallakar hoto State house
Image caption A watan Junairu Mr Jonathan ya ziyarci Maiduguri

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya ce "reshe ya juye da mujiya" a fafatawar da ake yi da kungiyar Boko Haram.

Lokacin da ya ke magana bayan kisan a kalla mutane ashirin da bakwai a wasu hare-haren na 'yan kunar-bakin-wake, Shugaba Jonathan ya ce lokacin makoki ne saboda kisan da ake yi babu kakkautawa yana gab da kawo karshe.

Ya ce "Sojojin Najeriya da na kasashe makwabta suna samun matukar cigaba a kokarin da suke yi na kwato yankunan da kungiyar Boko Haram ta mamaye a arewa maso gabashin kasar."

A watan da ya gabata, Najeriyar ta dage babban zaben da aka shirya gudanarwa da makonni shidda, tana cewar za ta bai wa sojoji lokaci na inganta sha'anin tsaro.

An soki lamirin shugaba Jonathan saboda gazawar sa ta kare farar hula daga wadannan hare-hare.