An gano makamai a wani gida a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yaro Hakkin mallakar hoto KDGH
Image caption Makwabta sun ce ba a mako guda, mota makare da akuyoyi da karnuka ba ta shiga gidan ba

Rundunar 'yan sanda ta Jihar Kaduna a arewacin Nigeria ta ce ta cafke wasu mutane shida wadanda aka samu makamai a gidansu, kuma akidarsu ta bambanta da ta mutanen yankin.

Kakakin rundunar, DSP Zubairu Abubakar, ya ce har yanzu suna neman jagoran mutanen, wadanda aka gano wasu ramuka masu kama da rijiya a gina nasu dake Kwanar Farakwai.

Makaman da aka gano a gidan dai sun hada da bindiga, da albarusai, da makamai na gargajiya; an kuma gano layu a gidan.

Bayanai dai na nuna cewa har ma mutanen, wadanda 'yan sanda ke zargin 'yan ta'adda ne, sun fara mallakar wasu gidaje da filaye a kusa da gidan nasu.

Hakimin gundumar Farakwai, Alhaji Muhammad Yaro, ya shaida wa BBC cewa wani yaro da aka daure da sarka a gidan ne ya samu kubuta, ya kuma kai rahoton abin da ke faruwa a gidan.

Shi ma wani mazaunin unguwar ya ce babu wanda ya taba ganin iyalan wadannan mutane, kuma ko sallar Juma'a ba sa zuwa, a cikin gida suke yin tasu.