Fulani sun koka da barayin shanu

Wani Bafulatani a wajen kiwo
Image caption Fulani sun dade su na kokawa da sace-sacen dabbobin da ake yi mu su.

A Najeriya a yayinda ake shirin zabe, al'ummar Fulani na cewa duk da tsarin mulkin dimokradiyya da ke gudana a kasar, su matsaloli ne suka dabaibaye su.

Sace-sacen Shanu, da rikice-rikice tsakanin Fulani makiyaya da manoma da kuma rikice rikice masu nasaba da addini da kabilanci na cikin matsalolin da Fulani ke cewa tsarin mulkin dimokradiyya bai kawar musu ba.

Wadannan matsaloli dai na janyowa fulani koma baya ta fuskar tattalin arziki, kamar yadda Alhaji Idiris Wakili Gundaro shugaban kungiyar Fulani Nagge dadi goma ya shaidawa BBC.

Ya kara da cewar barayin shanu na taka muhimmiyar rawa wajen hana musu kwanciyar hankali, saboda addabar su da suke yi da sace musu dabbobi.

Fulanin dai sun yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki domin share musu hawaye, domin su dai a yanzu ba su dan-dani romon mulkin dimukradiyya ba.