An gano asalin sunan 'Jihadi John'

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Ashe Jihadi John sunansa Mohammed Emwazi

An gano mutumin nan da aka fi sani da suna "Jihadi John" - da aka nuna yana wasa wuka a cikin faifen bidiyon da 'yan kungiyar I-S ke datse kawunan wadanda suka yi garkuwa da su.

BBC ta gano cewa sunansa na gaskiya Mohammed Emwazi.

Ya fito a cikin bidiyon da aka hallaka 'yan kasashen yamma da mayakan suka yi garkuwa da su--da suka hada da ba Amurken nan James Foley, da dan kasar Birtaniya Alan Henning da kuma dan jaridar nan dan kasar Japan, Kenji Goto.

An yi amanna cewa Emwazi dan asalin Biritaniya ne daga yammacin birnin London.