Minimah ya kai ziyara zuwa Baga

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Minimah ya jinjinawa dakarun Nigeria

Shugaban rundunar sojin kasa na Nigeria, Laftanar Janar Keneth Minimah ya kai ziyara garin Baga na jihar Borno domin yaba wa sojojin da suka yi aikin kwato garin daga hannun 'yan Boko Haram.

A lokacin ziyarar tasa, Janar Minimah ya sanar da yin karin girma ga sojojin da suka fafata da 'yan Boko haram a garin.

Bayanai sun nuna cewa Janar Minimah ya kai ziyarar ne domin kawar da duk wani shakku a kan ko sojojin Najeriya sun karbe garin na Baga daga hannun 'yan Boko Haram.

Janar Minimah ya ce akwai yiwuwar al'ummar yankunan da aka kwato daga hannun Boko haram su samu damar koma wa garuruwansu kafin zaben kasar da za a yi ranar ashirin da takwas ga watan Maris.

Dubban daruruwan mutane ne dai suka bar muhallansu sakamakon mamaye garuruwansu da kungiyar Boko Haram ta yi.

Janar Minimah ya kuma ce a yanzu sojojin kasar za su maida hankali ne wajen kwato sauran garuruwan da ke hannun Boko Haram wadanda suka hada da Gwoza da Madagali.