Ba za mu yarda a sake dage zabe ba - Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buhari na takara a karo na hudu a Nigeria

Dan takarar shugabancin Nigeria na jam'iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya ce ba za su yarda a kara jinkirta ranar zabukan kasar ba.

A hirarsa da BBC jim kadan bayan jawabinsa a Chatham House a London, Buhari ya ce kara daukar matakin sake dage ranar zabe zai saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

"Burinmu ne gaba daya a gudanar da zabe a ranar da aka saka cikin adalci ba tare da jinkirta ranar zabe ba," in ji Buhari.

Ya kara da cewar "Ba za mu yarda a kara dage zabe ba saboda hakan ya saba da kundin tsarin mulkin Nigeria."

A baya an shirya gudanar da zaben shugaban Nigeria ne a ranar 14 ga watan Fabarairu amma sai aka dage zuwa ranar 28 ga watan Maris saboda dalilan tsaro.

Janar Buhari zai fafata ne da Shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.