Nigeria: Mutane 25 sun mutu a hare-haren bam

Harin da aka kai a kusa da wata kasuwa a Jos Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A baya ma dai bama-bamai sun tashi a Jos, ciki har da wanda ya tashi a wata kasuwa

Rahotanni daga Jos, arewacin Nigeria na cewa bama-bamai uku sun tashi a wata tashar mota kusa da tsohon mazaunin Jami'ar Jos.

Wadanda suka shaida faruwar lamarin sun ce wadansu mutane ne da ke wucewa a mota suka jefa bama-baman, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 15.

A baya ma dai bam ya tattashi a birnin na Jos.

Wannan hari dai na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan tashin wadansu bama-baman a garin Biu na Jihar Borno a arewacin kasar, inda mutane kusan 10 suka rasa rayukansu.

Lamarin dai ya faru ne a kusa da wata tasha da ke wajen garin.

Wani wanda ya ce yana kusa da wurin lokacin da abin ya faru ya shaida wa BBC cewa 'yan kunar-bakin-wake ne mace da namiji suka tashi bama-baman.

A cewarsa, an tsayar da mutanen biyu ne a wani wuri inda aka shimfida tabarma ana binciken kayan duk wanda ya shiga garin, sai macen ta tashi bam din da ke jikinta, al'amarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama ya kuma raunata dan kunar-bakin wake na biyu.

Ihun da dan kunar-bakin-waken na biyu ya yi, yana neman taimako, inji mazaunin garin na Biu, ya sa mutane suka ruga wurinsa, amma da ya daga hannu sai aka ga bama-bamai a daure a jikinsa; hakan ya sa kowa ya ja baya.

Bayan 'yan mintuna ne sojoji suka isa wurin, suka harbi bam din sau biyu sannan ya tashi.

Ko a shekaranjiya Talata ma an kai hare-haren kunar-bakin-wake a biranen Kano da Potiskum.

Karin bayani