Obama da Netanyahu sun samu rashin jituwa

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Hayaniyar da ake yi tsakanin gwamnatin Obama da Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu ta kara tsamari a yayinda Mr Netanyahu ya zargi Amurka da sauran Shugabannin kasashen duniya da yin watsi da kokarin da suke yi na dakatar da yunkurin da Iran ke yi na kera makaman nukiliya.

A wani jawabi ga magoya bayansa a bayan birnin Kudus, ya ce alhaki ne da ya rataya ga wuyansa na kare abinda ya kira babbar barazanar da shirin nukliya na Iran ke yi.

A birnin Washington, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya daage kan cewar sasantawar nan da ake yi da Iran ta sanya Isra'ila zamowa wurinda ba shi da wata matsala ta tashin hankali

Karin bayani