An amince a sha wiwi don nishadi a Washington

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jihohin Alaska da Colorado da kuma Washington tuni suka amince da amfani da wiwi amma kadan

Birnin Washington DC na Amurka ya kasance wuri na baya-bayan nan a kasar da ya amince da amfani da tabar wiwi kadan.

Za a daina hukunta masu shan wiwi saboda nishadi idan dokar ta fara aiki a ranar Alhamis da tsakar dare.

Ko da yake har yanzu an haramta sayar da tabar ta wiwi.

Tun a watan Nuwambar da ta gabata ne dai aka amince da sauyin bayan wata kuri'ar rabagardama da gagarumin rinjaye.

Birnin Washington DC ba shi da cikakken 'yanci kamar sauran jihohi 50 na Amurka, domin majalisa ce ke da wani bangare na mulkinsa.

Kuma 'yan jam'iyyar Republican a majalisar ba sa so a yi sassauci ga dokar miyagun kwayoyi ta hanyar hana hanyoyin sanya haraji tare da sa ido kan tabar wiwin.