'Yan Boko Haram sun kai hari a Kala Balge

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lokacin da aka kai hare-haren babu jami'an tsaro a yankin

Rahotanni daga karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno da ke Nigeria na cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai jerin hare-hare kan kauyukan da ke yankin.

Maharan sun kai hare-haren ne a ranar Laraba, inda bayanai ke cewa sun kashe mutane fiye da dari.

Wani dan majalisar daga jihar Borno, Sanata Ahmed Zanna wanda ya tabbatar wa da BBC hakan ya ce, ba a samu labarin da wuri ba saboda rashin ingancin hanyoyin sadarwa.

Shi ma wani wanda ya tsere daga Balge ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun tara mutane suka ce za su yi muzu wa'azi, amma daga bisani suka harbe wasu.

Ya kuma kara da cewa maharan sun kewaye garin inda suka kyale mata da yara da ke kokarin tserewa, amma suka kashe maza da yaran da shekarunsu ba su fi 12 ba.