Ana gab da kawo karshen Boko Haram

Dakarun sojin Nigeria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kasashen Kamaru da Chadi da Nijar sun yunkuro dan taimakawa Nigeria dakile ayyukan mayaakn kungiyar Boko Haram.

Gwamnatin jihar Borno ta ce taron dangi da ake yi wa kungiyar Boko Haram tsakanin dakarun Nigeria da na kasashe makwabta zai taimaka wajen kawo karshen 'yan Boko Haram.

Sakataren gwamnatin jihar Borno, Ambasada Baba Ahmed Jiddah ya shaida BBC cewa, rashin mai da hankali tun farko shi ne abin da ya sa 'yan Boko Haram suka yi barna a yankin arewa maso gabas.

Ambasada Jiddah din kuma ya yi tsokaci kan batutuwa da dama da suka hada da zabe a jihar Borno da kuma alakar tsohon gwamna Ali Modu Sheriff da kuma gwamna Kashim Shettima.

Ambasada Jidda ya tabo batun yadda za a sake gina garuruwan jihar Borno da hare-haren mayakan Boko Haram suka daidaita, yace ana bukatar hada karfi da karfe tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Borno har ma da masu hannu da shuni domin farfado da jihar da ta shiga halin ni 'ya su.