Ya kamata Dasuki ya ajiye mukaminsa —NUD

Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Wasu kungiyoyi na ci gaba da sukar dage zaben Shugaban Kasa a Nigeria.

Wata hadakar kungiyoyi masu fafutukar tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya, mai suna Nigerians United for Democracy (NUD), ta bukaci mai bai wa Shugaban Nigeria shawara kan sha'anin tsaro, Kanar Sambo Dasuki ya ajiye mukaminsa.

Hadakar ta yi wannan kira ne a wajen wasu tarukan gangami da ta gudanar a Kano da Lagos da Abuja.

Ta yi zargin cewa Kanar Sambo Dasuki ne ya yi kutun-gwilar dage zaben kasar a kwanakin baya, saboda haka, bai kamata ya ci gaba da rike mukamin mai ba da shawara kan sha'anin tsaron ba.

NUD ta kuma bukaci 'yan Nigeria da su dage lallai sai an gudanar da zaben Shugaban kasar a ranar 28 ga watan Maris, da kuma zaben Gwamnoni a watan Afrilu.

Hadakar ta kuma ja hankalin 'yan Nigeria a kan mahimmancin yin amfani da katinan zabe na dindindin, sannan ta bukace su da su kasa, su raka, su kuma tsare bayan sun kada kuri'unsu.