Niger: Kassoum Moctar zai yi takara

Image caption CPR ta ce za ta tsayar da Muktar ne saboda ba a taba samun dan takara kasa da shekara 40 ba

A Jamhuriyar Nijar, jam'iyyar CPR-Inganci ta ce za ta tsayar da shugabanta, Kassoum Moctar, takarar shugabancin kasar a zaben shekarar 2016, duk da cewa yanzu haka yana tsare.

Jam'iyyar ta yanke wannan shawara ne a wajen wani taro da ta yi a Maradi.

Kakakin jam'iyyar, Halirou Issofou, ya shaida wa BBC cewa, "Mun tsai da kudurin cewa taro na gaba da za mu yi a Damagaram za mu tsai da dan takarar shugabancin kasa Kassoum Mamane Moctar a 2016 in Allah Ya kai mu, ganin cewa tun da ake Nijar ba a taba samun dan takarar shugabancin kasa da shekara 40 ba".

Da aka tambaye shi, ko ganin cewa Kassoum Moctar na tsare ne bisa zargin yin sama da fadi da dukiyar al'umma, ba sa tunanin za a ce suna yunkurin bai wa kura ajiyar nama? Sai ya ce:

"Mu mun yi imanin cewa tsoro ne ya sa aka yi garkuwa da shi; kuma muna da imanin kotun Nijar, in Allah Ya yarda...za su yi adalci, 'yan Nijar gabaki daya za su gane waye makaryaci..."

Ana dai tsare Kassoum Moctar, wanda tsohon magajin garin Maradi ne, saboda zargin sa da ake yi da laifin cin hanci da rashawa.