Rasha: Maci don jimamin mutuwar Nemtsov

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mutane sun ajiye kyandira da furanni a wurin da aka harbe Mista Nemtsov

Nan da 'yan sa'o'i kadan za a fara wani maci don jimamin mutuwar jagoran 'yan adawar nan na Rasha wanda aka bindige ranar Juma'a a Moscow.

Wadanda suka shirya macin sun ce suna sa ran mutanbe dubu hamsin za su taru a wata tashar da ke birnin na Moscow daga inda za su dunguma zuwa gadar da wani dan bindiga da ba san ko wanene ba ya harbe Mista Nemtsov.

An kafa wani karamin dandamali na jeka-na-yi-ka don tunawa da Mista Nemtsov a wurin, inda dubban mutane suka yi ta ajiye furanni da kyandira, da hotuna.

Gwamnatin kasar ta Rasha ta musanta zargin 'yan adawa cewa tana da hannu a kisan Mista Nemtsov.