APC ta zargi PDP da lalata allunan Buhari

A jihar Gombe da ke arewacin Najeriya, jam'iyyar APC mai adawa ta zargi gwamnatin jihar da kuma jam'iyyar PDP mai mulki da lalata manyan allunan yakin neman zabe na dan takararsu na shugabancin kasa, Janar Muhammadu Buhari.

Kazalika jam'iyar ta APC ta zargi gwamnatin PDP da kai wa magoya bayanta hari.

'Yan adawar dai na cewa jam'iyyar ta PDP na yin hakan ne domin huce haushinta game da alamar rauni da ta yi gabanin zabukan da aka shirya gudanarwa a wannan watan.

Sai dai jam'iyyar ta PDP ta musanta zargin, tana mai cewa saboda karfin da take da shi ba sai ta gallaza wa 'yan adawa ba kafin ta yi nasara.

A ranar 28 ga watan Maris ake shirin gudanar da zaben shugaban kasa kuma dukkanin jam'iyyun biyu na ci gaba da yakin neman zabe yanzu haka.