Yarinya a Chile ta nemi a bata maganin mutuwa

Hakkin mallakar hoto Valentina Maureira
Image caption Dokar Chile ta haramta amfani da kwayar maganin mutuwa

Shugaba Michelle Bachelet ta kasar Chile ta kai ziyara ga wata yarinya 'yar shkeara 14 a asibiti, wacce ta wallafa wani hoton bidiyo a intanet tana neman izinin a ba ta maganin da zai kashe ta.

Yarinyar mai suna Valentina Maureira ta na fama da wata cuta ce da ake gadonta wacce ke kama huhu da sauran sassan jiki.

Hoton bidiyon, wanda dubban mutane suka kalla, ya haddasa muhawara a kasar ta Chile a kan allurar da za a iya yiwa mutane su mutu, wacce dokar kasar ta haramta.

Mai magana da yawun Shugaba Bachelet ya ce burin Valentina ba zai cika ba, amma gwamnati za ta biya kudi don a kula da ita da mahaifanta.