Benjamin Netanyahu ya sauka a Amurka

Image caption Fira Minista Netanyahu zai yi jawabi ne kan adawarsa da cimma yarjejeniya da Iran

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyanhu ya sauka a Amurka, inda zai gabatar da wani jawabi mai cike da ce-ce-ku-ce a gaban Majalisar Dokokin kasar.

Jawabin na Mista Netanyahu zai mayar da hankali ne a kan adawar da yake yi da yiwuwar cimma matsaya a kan shirin nukiliya na Iran.

Tuni dai gabatar da jawabin, wanda zai yi ranar Talata, ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin Isra'ila da fadar gwamnatin Amurka ta White House, saboda jagororin jam'iyyar Republican ne suka gayyaci Mista Netanyahu ba da sanin Shugaba Barack Obama ba.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, John Kerry, ya kare tattaunawar da ake yi da Iran din, yana mai cewa yana fatan jawabin na Mista Netanyahu ba zai zama "wani gagarumin wasan kwallo na siyasa ba".

Ana sa ran Mista Kerry zai gana da Ministan Harkokin Wajen Iran ranar Litinin.