Ba ma goyon bayan Jonathan — wasu 'yan arewa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Goodluck Ebele Jonathan

Wasu kungiyoyi da daidaikun jama'a 'yan asalin arewacin Najeriya da ke zaune a kudancin kasar sun ce ba da yawunsu wasu suka bayyana goyon baya ga sake zaben shugaban kasar Goodluck Jonathan ba.

A ranar Asabar ne dai wasu 'yan asalin arewacin Najeriyar mazauna kudancin kasar suka gudanar da gangami a birnin Asaba na jihar Delta, inda suka yi da'awar cewa dukkanin 'yan asalin arewa da ke zaune a yankin na mara wa shugaba Jonathan baya.

Wasu 'yan arewar sun shaida wa BBC cewa wadanda suka ce suna goyon bayan takarar Jonathan din suna yi ne domin neman biyan bukatun kansu.

Sun kara da cewa masu ikirarin mara wa Jonathan din baya sun ari bakinsu ne kawai sun ci musu albasa domin babu wanda ya tuntube su.