Boko Haram ta fitar da bidiyon fille kan mutane

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo a shafinta na Twitter inda ta nuna wasu maza biyu da mayakanta suka fillewa kai.

Bidiyon wanda aka wallafa mai suna "yanka 'yan leken asiri" mai tsawon mintuna biyu ya nuna mayakan Boko Haram rike da mutanen biyu wadanda bayan an yi musu tambayoyi sannan aka yanke kansu.

Bisa bayanan da mutanen biyu suka bayar, kafin a yanke kawunansu, sun ce sun je garin Baga ne na jihar Borno domin ganin abin da ke faruwa a can sai mayakan Boko Haram suka kama su.

A bidiyon, wanda aka yi magana da harshen Hausa, an fassara kalaman a rubuce da harshen Ingilishi da Faransanci da kuma Larabci.

Wannan bidiyon da aka wallafa a Twitter ya kara nuna irin alakar kungiyar Boko Haram da kungiyar IS mai ikirarin jihadi.