Kamaru: Ana bi gida-gida ana allurar polio

Hakkin mallakar hoto LFRYDEPT STRUCTURAL BIOLOGYOXFORD

Ma'aikatar lafiya ta kasar Kamaru ta kara kaimi wajen bi gida-gida don diga wa yara 'yan kasa da shekaru biyar a duniya allurar riga kafin kamuwa da cutar shan inna, ko polio.

Ministan lafiya na Kamaru, Andre Mama Fouda, ya bukaci iyayen yara su bai wa jami'an kiwon lafiya goyon baya yayin da suke gudanar da aikin nasu.

Rubanya kokari a wannan aiki da ke gudana yanzu haka dai, ya biyo bayan sanarwar da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya bayar cewa kasar ta Kamaru ta ja da baya a jerin kasashen da suka yi nasarar shawo kan cutar shan inna a nahiyar Afrika.

Wakilin BBC a Kamaru ya ce sabbin kwayoyin cututtuka masu haddasa shan inna sun yadu a kasar ne sakamakon yawan 'yan gudun hijirar da suka shigo cikin kasar musamman daga Nigeria da kuma jamhuriyar tsakiyar Afirka ta gabashi.

Wannan lamari shi ne kuma ya maida hannun agogo baya a yakin da Kasar ta ke yi da cutar ta polio