Zamba wajen daukar 'yan sanda aiki a Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana kallon aikin dan sanda tamkar rabuwa ne da talauci

'Yan sanda a kasar Ghana sun tsare mutane biyar bisa zarginsu da hannu a cuwa-cuwar karyar daukar 'yan sanda 200 aiki.

Masu neman aiki galibinsu matasa maza, sun je cibiyoyi biyar a fadin kasar Ghana, saboda sakon da aka aika musu cewar an daukesu aikin dan sanda.

Mazambatar sun karbi kudi kusan cedi 2,000 zuwa cedi 3,500 inda suka yi wa matasan alkawarin samun aikin dan sanda.

Zamba da sunan ba da aiki ba sabon abu bane a kasar Ghana.

Galibin wadanda aka yi wa zambar talakawa ne, wadanda suka kosa su yi aiki.

Suna kallon aikin jami'an tsaro a matsayin wanda za su samu albashi babu matsala sannan ga gidan gwamnati kyauta.

Ministan harkokin cikin gidan Ghana ya yi alkawarin daukan hukunci a kan 'yan sandan da ke da hannu a wannan zambar.