Ana tafka kazamin fada a Tikrit na Iraki

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Dakarun gwamnati na samun goyon bayan mayakan sa-kai

Gwamnatin Iraki ta ce sojojinta suna fafatawa a wani gagarumin gumurzu domin sake kwato garin Tikrit.

A bazarar bara mayaka masu ikrarin jihadi na kungiyar IS suka kwace garin wanda ke zama cibiyar arewacin lardin Salahuddin.

Gwamnatin ta ce dakaru kimannin dubu talatin wadanda suka hada da mayakan sa kai 'yan sunni su kimanin dubu biyu tare da mayakan 'yan Shia da na Kurdawa sun durfafi garin na Tikrit tare da rakiyar jiragen yaki.

Bayanai sun ce a yanzu haka suna tazarar kilomita goma da tsakiyar birnin.

Firayi ministan Iraki, Haider al-Abadi, ya yi kira ga kwamandodin soji da su yi kokarin kaucewa fararen hula a lokacin hare-haren.