Shugaba Jonathan ya gana da 'yan takarar PDP

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Jam'iyyar PDP mai mulki na fuskantar kalubale daga jam'iyyar APC

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi wani taro da ilahirin 'yan takarar jam'iyyarsa ta PDP a dukkanin matakai daga jihohin kasar 36.

Taron, wanda aka gudanar da yammacin ranar Litinin a fadar Shugaban kasar ya mai da hankali ne kan hanyoyin da jam'iyyar za ta bi ta yi nasara a zabukan da ke tafe.

Jam'iyyar ta PDP wadda ke mulkin kasar tun daga 1999 na fuskantar barazanar da ba ta taba ganin irin ta ba daga babbar jam'iyyar adawa ta APC a yawancin jihohin kasar.

A ranar 28 ga watan Maris ne aka tsara gudanar da zaben Shugaban Kasa.