Benjamin Netanyahu zai yi jawabi a Amurka

Image caption Fira Minista Netanyahu zai yi jawabi ne kan adawarsa da cimma yarjejeniya da Iran

Fira Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, yana Amurka, inda ake sa ran zai yi amfani da wani jawabi da zai gabatar a gaban majalisar dokoki don nuna adawa da cimma yarjejeniya a kan shirin nukiliya na Iran.

Mista Netanyahu ya ce wannan ziyara ce mai dimbin tarihi, amma fadar gwamnatin Amurka ta White House ta fusata saboda ba a tuntube ta ba kafin a gayyaci Mista Netanyahu, da kuma adawar da fira ministan na Isra'ila ke nunawa ga duk wata yarjejniya da ba ta kunshi ruguza shirin nukiliya na Iran ba dungurungum.

Ana sa ran a yau sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, zai sake ganawa da ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif a Geneva.

Mista Kerry ya kare tattaunawar da ake yi da Iran din. Dangane da ziyarar ta Mista Netanyahu kuma ya ce: "Ba za mu so mu ga an mayar da wannan al'amari wani gagarumin wasan kwallo na siyasa ba. A zahiri abu ne bambarakwai a ce daga kakakin majalisar wakilai muka samu labarin wannan ziyara".

Karin bayani