Tanzania ta hana kashe zabiya.

Wani yaro zabiya a Tanzania Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani yaro zabiya a Tanzania

Mista Kikwete ya ce camfin da ake yayatawa kan amfani da bangarorin jikinsu don samun sa'ar rayuwa bashi da tushe kuma hakan na kara ingiza masu aiwata da ta'asar.

Ana sayar da bangarorin jikin zabiya kan daruruwan daloli a Tanzaniya saboda an yi amanna su na kawo sa'a a kasuwanci da siyasa da soyayya.

Masu fafutuka sun ce an kashe fiye da zabiya 70 a kasar cikin shekaru kadan da su ka gabata.

A farkon shekarar nan ne dai gwamnati ta dakatar da bokaye in da ta ce su na daga cikin ma su zuzuta wutar lamarin