Biritaniya za ta fito da tsarin dauri kan watsi da zargin lalata

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rahoton ya biyo bayan binciken da aka yi bayan daure wasu mutane bakwai da aka samu da laifin lalata yara

Firai ministan Biritaniya, David Cameron na shirin fito da wani tsari na daure malaman makarantar da suka yi watsi da zargin fyade.

Shirin zai kuma shafi da ma'aikatan da ke kula da jin dadin jama'a da wasu jami'an gwamnati, inda za su fuskanci dauri har na tsawon shekaru biyar a gidan kaso.

Ana yawan samun gungun mutane da zargin lalata da kananan yara a kasar.

Haka na zuwa ne a daidai lokacin da wani rahoto ya bayyana cewa akalla akwai yiwuwar yara mata 370 ne aka lalata a gundumar Oxfordhshire a cikin shekaru 16 da suka wuce.

Rahoton dai ya ce wadanda abin ya shafa sun ce ba a yarda da abin da suke fada idan sun kai korafi ga hukumomi.

Ko kuma ma a dauka da yardarsu aka tara da su.