''Yan sandan Amurka na nuna wariyar launin fata'

Hakkin mallakar hoto
Image caption A bara ne aka kashe wani bakar fata a Amurka wanda ba ya dauke da makami

Wani bincike da ake gudanarwa a kan kisan wani saurayi bakar fata da wani dan sanda farar fata ya yi bara a Ferguson na jihar Missouri ya bankado hujjoji masu dimbin yawa cewa 'yan sanda da jami'an kotu a garin na nuna wariyar launin fata.

Rahotanni daga Amurka sun ce idan aka wallafa shi, binciken na Ma'aikatar Shari'a ta kasar zai zargi rundunar 'yan sanda da yin amfani da karfi fiye da kima a kan bakaken fata.

Kisan Michael Brown a watan Agustan bara ya haddasa tashin-tashina a kasar ta Amurka, inda aka kwashe makwanni ana zanga-zanga.

Fitaccen mai rajin kare hakkokin dan-Adam din nan Reverend Jesse Jackson ya ce rahoton ya kara fitowa da bambance-bambancen da ke tsakanin al'ummar Amurka fili.