Jega: Majalisar wakilai ta gargadi gwamnati

Image caption Mr Jonathan ya musanta zargin yanason cire Jega

Majalisar wakilan Nigeria ta zartar da shawarar dakile duk wani yunkuri na cire shugaban hukumar zaben kasar, Attahiru Jega daga mukaminsa.

Majalisar ta zartar da shawarar ce, bayan da Ali Ahmed, dan majalisa daga jihar Kwara ya gabatar da kuduri kan batun shugaban INEC din.

A cewar Majalisar duk wani shiri na raba Jega da kujerarsa tamkar neman janyo yamutsi ne a kasar a don haka gwamnati ta bar shi a kan kujerarsa har zuwa bayan zabe.

Tun a karshen mako ne jaridun Nigeria suka wallafa rahotannin da ke cewar fadar shugaba Jonathan na shirin tilastawa Jega tafiya hutu kafin ranar zabe.

Bisa jadawalin hukumar INEC, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a ranar 28 ga watan Maris, sai kuma zaben gwamnoni a ranar 11 ga watan Afrilu.