An yi jana'izar Nemtsov a Moscow

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Magoya bayan Nemtsov sun yi jimamin rasuwar

A birnin Moscow na Rasha, dubban masu makoki ne su ka yi wa gawar jagoran 'yan adawa, Boris Nemtsov, wanda aka harbeshi a kan wata gada kusa da fadar gwamnatin kasar ranar Juma'a da daddare, bankwana.

An binneshi a wata makabarta da ke kudu ma so yammacin Moscow.

Wasu 'yan siyasa a nahiyar Turai sun ce Rasha ta hana su shiga kasar don halartar jana'izar.

Marcin Zaborowski shi ne daraktan cibiyar al'amuran kasa da kasa na Poland:

Ya ce "An hana mu izinin shiga kasar amma an shaida wa kakakin majalisar dokokinmu cewa hakan tamkar ramuwa ce kan takunkumin da aka kakabawa kakakin majalisar dattijan Rashar."

Kungiyar tarayyar turai ta yi tir da abin da Rashar ta aikata.

Fadar gwamnatin kasar ta tura wakilin shugaba Putin a majalisar dokokin Rasha Garry Minkh, don halartar jana'izar a madadinta.