Matasan Naija Delta na neman hadin kai a arewa

Image caption Nigeria na tunkarar manyan zabubbuka

Wasu matasa na yankin Naija Delta da ke kudancin Nigeria na ziyarar takwarorin su na arewa ,domin abinda suka ce neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokaci da kuma bayan zabe.

A lokacin ziyarar Shugaban kungiyar matasan ta 'yan kabilar Ijaw ya nisanta kansu da rahotannin dake cewa sun ce za su tayar da rigima idan har Shugaba Goodluck Jonathan bai ci zabe ba.

Ya kara da cewa mummunar fassara aka yi musu.

A saboda haka suka ce makasudin ziyarar da suke yi a arewacin Nigeriar shi ne neman zaman lafiya a lokaci da kuma bayan zabe

To sai dai a cewar wasu kungiyoyin matasan arewacin Nigeriar wannan ziyarar na da kanshin siyasa

Malam Aminu Adam shi ne sakataren kungiyar matasan arewa ta ACAC, ya kuma fadawa BBC cewa 'idan dai batun zaman lafiya ne, mu mun karbe shi amma idan batun siyasa ne ko maganar dan- takara, to mu ba ruwanmu da wannan al'amari'.