Karancin mai na kara tsanani a Nigeria

Image caption Gidajen mai kalilan ne ke sayarwa, kuma a wurare da dama farashi ya karu

Matsalar karancin man fetur a sassan Najeriya daban-daban na kara kamari, inda layukan motoci ke kara tsayi a gidajen mai.

A manyan biranen kasar irin Kano, da Abuja, da Lagos, gidajen mai kadan ne ke sayar da man.

Dillalan man masu zaman kansu dai sun musanta zargin da ake yi cewa su ne suke haddasa karancin man.

A cewar Alhaji Bashir Ahmad Danmalam, shugaban kungiyar dillalan a Jihar Kano, abin ya fi karfinsu, matsalar "daga sama take".

Ya ce a farashin gwamnati, kamata ya yi su sayi man a kan naira 77.66, amma ba sa samu a hakan.

"...Wajen naira 80 muke sayen shi, yanzu sai ya koma naira 92 a Lagos inda muke sayo shi. Saboda haka sai muka ga ba za mu iya ba—in mun saye shi a kan naira 92 zai zo mana nan a kan naira 110 zuwa 115", inji Alhaji Bashir.

Shugaban dillalan man ya kara da cewa da suka nemi jin dalilin da ya sa farashin ya karu, "sai suka gaya mana [cewa] a da [ana sayen dalar Amurka] a kan naira 155, ta koma 158, yanzu ta koma 199".

Kamfanin man fetur na kasa wato NNPC ya ce ya samar da kari a kan adadin man da ya saba samarwa don ganin ya wadata, sai dai kuma mai yiwuwa saboda abin nan da masu iya magana kan ce 'in dambu ya yi yawa, ba ya jin mai', har yanzu dai babu alamun samun saukin layukan man.