APC ta dora alhakin matsalar fetur a kan Jonathan

Image caption APC ta ce gwamnatin Jonathan ta sace kudin gas $12bn

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, APC, ta ce ana fama da wahalar fetur ne saboda zargin da ta yi cewa gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan ta sace $12bn da aka ware domin karfafa wa mutane gwiwa su rika amfani da gas a harkokinsu na yau da kullum.

Kazalika, jam'iyyar ta ce wahalar man fetur din na da nasaba da rashin biyan masu kwangilar shigo da man kudinsu.

Wata sanarwa da kakakin jam'iyyar, Alhaji Lai Mohammed, ya fitar ta ce gwamnatin shugaba Jonathan na so ne ta kawar da hankulan 'yan kasar daga ainihin dalilan da suka jawo matsalar man fetur din, shi ya sa ma ta dora alhakin hakan kan jam'iyyar adawa.

Ya kara da cewa duk da alkawarin da ministar kudin kasar, Ngozi Okonjo-Iweala , ta yi a watan Fabrairu cewa za ta biya masu shigo da man kudinsu, N264 bn, a wancan lokacin, ta gaza yin hakan saboda an sace kudin.

Jam'iyyar ta APC ta ce ta yi mamakin yadda gwamnatin PDP ke bari 'yan kasar na shan wahalar rashin mai duk da kudin da ke karkashinta.