Ebola: Saliyo za ta karbi tallafin kudi daga IMF

Hakkin mallakar hoto AP

Asusun ba da lamuni na duniya, IMF, ya amince da wani tallafin kudi na dala miliyan 187 ga Saliyo bayan da annobar cutar Ebola ta hallaka mutane fiye da dubu uku a kasar

Za a bai wa kasar ta Saliyo fiye da dala miliyan takwas daga cikin kudin nan take.

Wani jami'in asusun na IMF ya ce annobar da kuma faduwar farashin tama a kasuwannin duniya sun yi mummunan tasiri a kan tattalin arzikin kasar.

A yau Talata shugabannin kasashen Saliyo, da Liberia, da Guinea za su halarci wani taron koli a Brussels da nufin hada karfi da karfe a yunkurin kawar da cutar ta Ebola dungurungum.