'Yan sandan Ferguson na nuna wariya —Bincike

Hakkin mallakar hoto no credit
Image caption Kisan Michale Brown a watan Agustan bara ya haddasa zanga-zanga a fadin Amurka

Jami'an ma'aikatar shari'a ta Amurka sun ce binciken da suka gudanar a kan kisan wani saurayi bakar fata da wani dan sanda farar fata ya yi bara a Ferguson na Jihar Missouri ya bankado hujjoji da dama cewa 'yan sanda da jami'an kotu na nuna wariyar launin fata a garin.

Rundunar 'yan sandan garin ba ta ce komai a kan rahoton ba, wanda ake sa ran wallafawa nan ba da jimawa ba, sai dai wata 'yan kwamitin gudanarwar jam'iyyar Democrat daga garin ta ce tana sane da dokokin da ake aiwatar a garin nata masu nuna wariyar launin fata.

Kisan Michael Brown a watan Agustan bara ya haddasa tashin-tashina a kasar ta Amurka, inda aka kwashe makwanni ana zanga-zanga.

Fitaccen mai rajin kare hakkokin dan-Adam din nan Reverend Jesse Jackson ya ce rahoton ya kara fitowa da bambance-bambancen da ke tsakanin al'ummar Amurka fili.

Karin bayani