Kamfanin Areva ya yi asarar $5bn

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamnatin Faransa ta ce ba za ta kara wa Areva kudi ba sai ya yi bayani kan dabarun kasuwancinsa

Kamfanin Faransa da ke samar da makamashin nukiliya, Areva, ya ce ya yi asarar fiye da $5bn a bara.

Kamfanin dai yana hakar ma'adinin uranium a Jamhuriyar Nijar.

A wata sanarwa da ya fitar, kamfanin ya ce zai rage kudin da yake kashewa da kimanin $1bn a cikin shekaru biyu, kana ya mayar da hankali sosai wajen samar da makamashin nukiliya.

Kamfanin ya kashe shekaru hudu yana yin asara, kuma a ranar Talata ministan tattalin arzikin Faransa, Emmanuel Macron, ya ce gwamnati za ta kara masa kudi ne kawai idan kamfanin ya yi gamsasshen bayani dangane da dabarun kasuwancinsa.