Cutar Ebola ta ragu a kasar Liberia

ma'aikatan lafiya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar Ebola ta lakume rayukan dubban mutane a yammacin Afurka.

Hukumar lafiya ta duniya tace an samu raguwar wadanda suka kamu da cutar Ebola a kasar Liberia a makwan da ya wuce.

Sai dai an samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar da 132 a kasashen Guinea da kuma Saliyo, adadin da ya rubanya wanda ake da shi sau hudu a makwannin da suka wuce.

A rahoto na baya-bayan nan da hukumar lafiya WHO ta fitar kan barkewar cutar Ebola a yammacin Afurka, tace an samu karuwa a adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar a kasashen Guinea da Saliyo.

WHO tace a wadannan kasashe ba a kebe wadanda suka kamu da cutar da gaggawa, haka kuma ba a fahimci yadda za a yi wa masu dauke da cutar magani ba.

Ya yin da hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya tace har yanzu ana ci gaba da binne gawawwakin wadanda suka mutu ba bisa ka'aida ba.

Cutar Ebola dai ta hallaka mutane fiye da 10,000 a yammacin Afurka, inda cutar ta fi kamari tare da yin barna a kasashen Liberia, da Guinea da kuma Saliyo.

Ya yin da kasashen Senegal da Nigeria da Mali suka kakkabe cutar daga cikinsu baki daya.