Mun raba kashi 80 na katunan zabe — INEC

Image caption INEC ta ce a makon gobe za ta gana da jam'iyyu.

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta yi ikirarin cewa ta raba kashi 80 cikin 100 na katunan zabe na dindindin ga masu zabe.

A wani taron manema labarai da hukumar ta kira, Kwamishinan hukumar, Chris Iyimoga ya kara da cewa sun kammala karbar takardu da akwatunan zabe daga 'yan kwangilar da aka bai wa aikin yin su.

Ya ce "Mun raba katunan zabe na dindindin guda 55,232,875, watau hakan na nufin mun raba 80 cikin 100."

Mr Iyimoga ya ce hukumar ta yi gwaji sosai kan na'urar da ke tantance sahihancin katunan zabe, watao card reader, yana mai cewa sun tabbatar za ta yi aiki ba tare da wata matsala ba a lokutan zaben.

A cewarsa, INEC za ta gana da manyan jami'anta na jihohi da kuma wakilan jam'iyyu a makon gobe domin shaida musu irin shirye-shiryen da ta yi a game da zaben 2015.