'Yan ta'adda sun kwace rijiyoyin mai a Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rijojin sun kasance a rufe na tsawon makonni saboda tashin hankalin da ake yi a yankin

Rahotanni sun ce mayakan sa kai masu tsattsauran ra'ayin addinin Musulunci a Libya sun kwace rijiyoyin man fetur biyu.

Hakan ya biyo bayan karewar harsasan dakarun da ke gadin rijiyoyin mai na al-Bahi da al-Mabrouk a tsakiyar kasar, abin da yasa suka janye.

Wasu kungiyoyin mayakan da ba sa ga maciji da masu tsattsauran ra'ayin na ci gaba da gwabza fada a yunkurin kwace iko da kasar.

Su ma dakarun da ke biyayya ga gwamnatin kasar biyu wadanda ke fada da juna sun kaddamar da hare-hare ta sama a kan juna, har ma an ba da rahoton kai hari a kan tashoshin jiragen ruwan daukar mai biyu da filin jirgin sama na Tripoli.

Majalisar Dinkin Duniya na yunkurin farfado da tattaunawa da nufin kawo karshen fadace-fadacen da suka dabaibaye kasar ta Libya, tun bayan kifar da gwamnatin Kanar Mu'ammar Gaddafi a shekarar 2011.