Bam ya hallaka sojin Nijar biyu a Diffa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Nijar na sintiri domin kawar da Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun hallaka sojin Jamhuriyar Nijar biyu tare da raunata daya a wani harin bam a kusa da garin Diffa da ke Kudu maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar sojin Nijar, Kanar Ledru Mustapha wanda ya shaida wa BBC cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe tara da rabi na safiyar ranar Laraba.

A cewarsa, 'yan Boko Haram din sun ajiye bam dinne a kan hanya sannan suka tayar da shi daga nesa.

Sai dai Kanar Mustapha ya ce sun kashe 'yan Boko Haram din su biyu da suka tayar da bam din.

Dakarun kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi sun hada gwiwa domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 a Najeriya.