Mutane 33 sun mutu a mahakar kwal a Ukraine

Image caption Ba a fiye samun matsala a wuraren hakar ma'adinan Ukraine ba

Mutane akalla 33 ne suka mutu a lokacin da wani abu ya fashe a wata mahakar ma'adinin kwal da ke Donetsk a gabashin Ukraine.

Yankin na Donetsk dai na hannun 'yan tawaye ne masu goyon bayan Rasha.

Wasu jami'an 'yan tawayen sun shaida wa BBC cewa ya zuwa yanzu an gano gawarwakin mutane bakwai.

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Laraba, sakamakon matsalar na'ura.

Kazalika, ana ganin cewa ginin ya danne kimanin mutane 30, sai dai ma'aikatan ceto na kokarin fito da su.

Ba kasafai ake samun hatsarin da ya danganci wuraren hakar ma'adinai a Ukraine.