IS sun sake lalata kayan tarihi a Iraqi

Mayakan kungiyar IS Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu da'awar kafa daular musulunci a kasashen Iraqi da Sham sun ce gumakan da suka lalata sun sabawa koyarwar addinin musulunci.

Hukumomi a Iraqi sun ce mayakan kungiyar IS suna rusa birnin Nimrud mai dimbin tarihi na daular Assyria a kasar ta Iraqi.

Ma'aikatar dake kula da kayan tarihi da yawon bude ido ta ce masu jihadin suna amfani da manyan makamai wajen lalata birnin Nimrud.

An kafa birnin ne a karni na 13 kafin zuwa Annabi Isa kuma yana kusa ne da kogin Tigris dake dab da Mosul.

A watan da ya gabata, kungiyar IS ta fitar da wani hoton video dake nuna mayakan ta suna rusa kayan tarihi a wani wurin kayan dake birnin Mosul. Masu jihadin dai sun ce kayayyakin gumaka ne da suka saba ma addinin Musulunci.