Za a dinga hutun makaranta ranar Sallah a New York

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Bill de Blasio ya ce ya dauki matakin ne saboda a mutunta addinnin kowa

Magajin garin birnin New York na Amurka, Bill de Blasio ya ce daga shekara mai zuwa za a dinga rufe makarantun gwamnati a lokutan Idi.

A cewar magajin garin, daga shekarar karatu ta 2016, dalibai ba za su je makaranta ba a ranar Eid al-Adha da kuma Eid al-Fitr.

Mr de Blasio ya ba da sanarwar ce a shafinsa na Twitter.

Abin da hakan ke nufi shi ne daga yanzu ranar bukukuwar Musulmi na cikin a kalandar karatu a birnin New York a matsayin ranakun hutu.

Sanarwar ta yi wa al'ummar Musulmi dadi kasancewar za su yi bukukuwar Sallah tare da 'ya'yansu sabannin yadda lamarin yake a baya.