'Abin da ke tsakani na da mataimaki na'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamna Muazu Babangida Aliyu

Dangantaka tsakanin gwamnan jihar Niger, Mu'azu Babangida Aliyu da kuma mataimakinsa Alhaji Ahmed Ibeto ta kara tsami bayan gwamnan ya sa an fitar da ofishin mataimakinsa daga cikin fadar gwamnatin jihar.

Rashin jittuwar dai ta samo asali ne tun watan Janairu lokacin da mataimakin gwamnan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Gwamna Babangida Aliyu ya musanta zargin cewar an sauya wa mataimakin gwamna ofis ne saboda a yanzu ba sa ga maciji.

"Sauranmu wata uku dole ne a soma gyare-gyare, wasu za su ce domin ya fita PDP ne, amma shi (Ibeto) ya san cewar ana gyare-gyare," in ji Aliyu.

Sai dai kakakin mataimakin gwamnan, Mr Jonathan Vatsa ya ce "Hujjar da suka bayar shi ne za su gyara ofis din, amma mataimakin gwamna bai ce yanason a gyara masa ofis ba."

A baya dai gwamna ya mika ragwamar mulki jihar ga kakakin majalisa lokacin da zai yi wata tafiya a maimakon mataimakin nasa; kuma ya bukaci da ya fice daga zauren da ake taron majalisar zartarwar jihar na mako-mako.