An ba da umurnin a tono gawar Sankara

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Sankara na da farin jini a Burkina Faso

Gwamnatin Burkina Faso ta ba da umurnin a tono gawar tsohon shugaban kasar, Thomas Sankara daga wata makabarta da ke gabashin babban birnin kasar Ouagadougou.

Sai dai iyalan gidan margayi Sankara sun ce suna da shakku ko za a iya gano gawar.

An kashe Mr Sankara ne a shekarar 1987 a lokacin juyin mulkin soja inda tsohon abokinsa Blaise Compaore ya gaje shi har zuwa watan Oktoban bara.

Sabuwar gwamnatin kasar karkashin jagorancin Michel Kafando ta yi alkawarin duba lamarin lokacin da ya hau mulki a cikin watan Nuwamba.