Ana zargin sojojin Somalia da yi wa al-shabab aiki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kori mayakan al-shabab daga Mogadishu

Hukumomi a kasar Somalia sun tsare manyan sojoji tara da ake zarginsu da yi wa kungiyar al-Shabab aiki.

Ana zargin sojojin da taimaka wa mayakan al-shabab a harin da suka kai a wani babban otal a Mogadishu babban birnin kasar a watan Junairu.

A lokacin da aka kai harin, akwai wasu jami'an kasar Turkiya wadanda ke jiran isowar shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Mutane uku ne suka mutu sakamakon harin.

Gwamnatin Somali tare da hadin gwiwar dakarun kasashen Turai sun shafe shekaru suna yaki da kungiyar al-Shabab.