Kura ta lafa bayan sabon rikici a Taraba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An kona masallatai da coci-coci a rikin ranar Alhamis

Rahotannin daga garin Tella a karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba na cewa kura ta lafa bayan tashin hankalin da ya sake barkewa a ranar Juma'a.

Tashin hankali mai nasaba da kabilanci da addini ya kai ga asarar rayuka da jikkata baya ga kone-konen gidaje a garin.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba, DSP Joseph Kwaji, ya tabbatar wa da BBC batun sake barkewar tarzomar, amma yace a yanzu kura ta sake lafawa.

Ko da yake dai kawo yanzu babu takamaiman adadin mutane da suka rasa rayukansu a sabon tashin hankalin, to amma wani mazaunin garin na Tella, Malam Lawal, ya ce ya ga gawawwakin mutane akalla biyar.

A tashin hankali da aka yi jiya a garin naTella dake karamar hukumar Gassol, an tabbatar da mutuwar akalla mutum guda da jikkata wasu da dama, baya ga kona masalllatai da majami'u da gidajen jama'a da shagunan 'yan kasuwa da masu yawan gaske.

Bayanai sun ce rigimar ta taso ne sanadiyyar wata takaddama tsakanin wasu matasa mashayan tabar wiwi, amma kasancewar su daya dan kabilar Jukun kuma kirista da kuma Bahaushe musulmi, sai lamarin ya dauki salo na kabilanci da addini.

Jihar ta Taraba dai ta sha fama da munanan rigingimu masu nasaba da kabilanci da kuma addini, musaman a kananan hukumomin Wukari da Ibi kuma a baya-bayan nan karamar hukumar Gassol, inda garin na Tella yake.