Lalata kayan tarihin Nimrud laifukan yaki ne - UNESCO

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A birnin Mosul, mayakan IS sun lalata gumaka da suka ce ya saba wa addinin Musulunci

Hukumar raya ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana lalata dadaddun kayan tarihi na daular Assyria da ke birnin Nimrud da mayakan kungiyar IS suka yi a matsayin laifukan yaki.

Jami'an Iraqi sun ce an yi amfani da katafila wajen rushe katangu da dadaddun sassake-sassake da suka kai kimanin shekaru dubu uku.

Birnin na Nimrud, babbar cibiya ce da ke kunshe da tarihin ci gaban Syria, an ambato shi a cikin littafin bible.

Akan haka ne ma, gwamnan birnin Kirkuk na kasar Iraqi, Najmaldin Karim ya bayyana cewa lalata kayan tarihin da IS ta yi tamkar kaddamar da yaki ne a kan salon rayuwar jama'a.

Nineveh Yakou wata malamar tarihi ce da ta kware wajen kare al'adun kasar Iraqi.

"Nimrud wani birni ne da ke da matukar muhimmanci ga kasashen duniya ta wane bangare, an raba mu da irin wannan tarihi, kuma babu wanda zai iya sake ganowa. Wannan abin damuwa ne ga daukacin duniya."

Kawo yanzu dai kungiyar ta IS bata bayyana dalilanta na lalata kayan tarihin na Nimrud ba.