Bama-bamai sun tashi a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bama baman sun tashi a sassa daban daban na Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya sun ce bama-bamai sun tashi a sassa daban-daban na birnin, sun kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Bama-baman sun tashi ne a Tashar motar Baga, da kasuwar Monday Market, da kuma tashar Borno Express duka a birnin na Maiduguri.

Rahotanni sun ce bam daya ya tashi a Tashar Baga, yayin da bama-bamai biyu suka tashi a kasuwar Monday Market, biyu a tashar Borno Express.

Ana dai kyautata zaton 'yan kunar-bakin-wake mata ne suka tashi bama-baman.

Tun bayan da hukumomin tsaro a Najeriyar suka kuduri aniyar kawar da barazanar 'yan kungiyar Boko Haram, tashe-tashen bama-bamai ke karuwa a sassan arewacin kasar daban-daban.