Shekau ya yi mubaya'a ga IS

Jagoran Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto
Image caption An dade ana diga alamar tambaya, game da alakar da ke tsakanin Boko Haram da kungiyar IS ta fuskar ayyukansu.

Kungiyar Boko Haram ta sanar da yin mubaya'a ga kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci IS a wasu yankunan Iraki da Syria.

Sakon da kungiyar ta Boko Haram ta fitar wanda ke dauke da muryar shugaban ta, Abubakar Shekau yana ikirarin yin mubaya'a ga kungiyar IS, a iya cewa ya kawo karshen tababar da wasu su ke yi akan ko akwai alaka tsakanin kungiyoyin biyu.

A cikin sakon, ana jin Abubakar shekau yana magana da larabci, yayin da ake fassara abinda yake fada a rubuce da turanci da kuma Faransaci.

Inda ya ce su na sanar da mubaya'ar su ga shugaban IS, Khalifa Ibrahima dan Awwaad, wanda aka fi sani da Abu Bakr al-Baghdadi, za kuma su rika jin maganar sa, tare da yi masa biyayya, a cikin abin so da abin ki, cikin sauki da tsanani, kuma ba za a yi masa jayayya ba sai cikin lamarin da ya sabawa addinin musulunci.

Tuni dama Abu Bakr al-Baghdadi ya amince da mubaya'ar da wasu kungiyoyin da'awar jihadi daga gabas ta tsakiya, da Afghanistan, da Pakistan da kuma arewacin Afrika su kayi wa kungiyar ta IS.

Kafin wannan lokaci dai, kungiyar Boko Haram ta rika yin wasu abubuwa da ke alamta alaka da kungiyar IS, ko dayake babuwata babbar alama da ta fito fili kafin yanzu.

Irin kwarewa da kungiyar ta Boko Haram ke nunawa wajen harhada faya-fayen bidiyonta, da amfani da shafin Twitter wajen wallafa bidiyon ayyukanta, da kuma shi kanshi wannan sakon dake dauke da muryar Abubakar Shekau, alamu ne da ke nuna cewa kungiyar ta Boko Haram tana koyi, ko samun taimakon kwararru daga IS, domin kuwa, ayyukan nata, sun koma daukar salon na IS.

Hakan ne yasa wasu ke tunanin akwai alaka a tsakaninsu, amma wasu ke ganin kungiyar ta Boko Haramce kurin ke yin gaban kanta, batare da IS din tasan tana yi ba, duk kuwa da cewa wani kusa a IS da ya kware a fannin sadarwa Abu Malik Shayba, ya yi ikirarin yin hulda da shugabannin Boko Haram.

Yanzu dai wani abu da zai kara tabbatar da wannan dangantaka, shi ne, idan Abu Bakr al-Baghdadi, shugaban kungiyar IS, ya amince da mubaya'ar ta Boko Haram, kamar yadda a kaga ya yi wa wasu kungiyoyin jihadi masu akida irin tasu.